Nafisa Abdullahi ta tabbatar da kanta a matsayin jarumar da ba ta damu da kalaman mutane ba, inda take ci gaba da gudanar da rayuwarta yadda take so. Wannan halin nata ne ya sa take ci gaba da kasancewa daya daga cikin jaruman da ake yayi a masana'antar Kannywood.
Wani lokacin masoya sukan yi mata tambayoyi cikin zolaya kamar "ina dankwalinki?" idan suka ga ta yi shigar da ba su saba gani ba.
Hotunanta sanye da kaya irin na zamani, kamar wando ko riga ba tare da dankwali ba, sukan janyo tsokaci daga masoya, inda wasu ke mata barkwancin cewa "ta kusa zama 'yar America".
Shahararriyar jarumar fina-finan Hausa, Nafisat Abdullahi, ta kasance daya daga cikin jaruman da suka fi daukar hankali a shafukan sada zumunta saboda salonta na daban da kuma kusancinta da mabiyanta. A kwanakin nan, wasu hotunanta sun janyo maganganu daban-daban, inda wasu masoya suka rika tsokanarta cikin raha, yayin da wasu kuma suka bayyana sha'awarsu ga yanayin shigarta. Yanayin Hotunan Da Suka Jawo Hankali
Dayawa daga cikin masoyanta suna yaba fatarta ta "black beauty" da rashin amfani da mayukan bleching.